Asabar 17 Oktoba 2026 - 21:07
Nasarar Matasan Iran a Gasar Ƙasa da Ƙasa Na Ƙara Ƙarfafa Fatan Makoma Mai Haske

Hauza/ Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i, ya taya tawagar ƙasar Iran ta kokawar gargajiya, ’yan ƙasa da shekaru 23, murnar lashe gasar zakarun duniya da aka gudanar a Amurka, inda ya bayyana bajintar matasan ƙasar a fagen wasannin duniya a matsayin abin da ke ƙarfafa fatan samun makoma mai haske.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Ayatullah Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i ya aike da saƙon taya murna ga tawagar ƙasar Iran ta kokawar gargajiya ta ’yan ƙasa da shekaru 23, bisa nasarar da ta samu a gasar zakarun duniya.

Ga fassarar saƙon da Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya fitar:

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Ina taya ’yan wasan tawagar ƙasar Iran ta kokawa irin ta gargajiya ta ’yan ƙasa da shekaru 23 murnar lashe gasar ƙasa da ƙasa ta matasa masu fatan zama zakarun duniya, wadda aka gudanar a Amurka. Haka kuma, ina taya masu horar da ’yan wasan, waɗanda suka yi ƙoƙari matuƙa, da daukacin al’ummar Iran wannan nasara mai cike da alfahari.

Bajintar matasan ƙasarmu, ɗaga tutar Iran cikin farin ciki da kuma rera taken ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fagage daban-daban na duniya, duk suna haskaka fatan al’ummar ƙasar ga matasansu wajen cimma makoma mai haske da ɗaukaka.

Ina addu’ar Allah Ya taimaki daukacin matasan Iran abar alfahari a dukkan hanyoyinsu.

Sayyid Mujtaba Husaini Khamene’i

25 Mehr 1405 (17 Oktoba 2026)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha